in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar Barcelona na fatan amfani da kwallon kafa wajen bunkasa zaman lafiya a tsakanin Palesdinu da Isra'ila
2013-08-16 15:35:18 cri

Daga nan ne kuma membobin kungiyar suka isa fadar shugaban kasar Isra'ila dake birnin Kudus, inda shugaba Shimon Peres, da firaministan kasar Binyamin Netanyahu suka gana da su. Shugaba Peres ya bayyana cewa, ziyarar kungiyar Barcelona ta cimma burin matasa da yaran kasar, Ta kuma bada gudummawa wajen yunkurin da ake yi na wanzar da zaman lafiya a tsakanin al'ummun Palesdinu da na Isra'ila.

Daga nan sai ya bayyana fatansa, na kallon wasannin kwallon kafa masu ban sha'awa da kungiyar zata buga, da burin habaka shirin wanzar da zaman lafiya, kana yayi fatan masu sha'awar kungiyar Barcelona za su ziyarci kasar ta Isra'ila don yawon shakatawa.

Da yake mai da jawabi, shugaban kungiyar Barcelona Rosell ya ce, al'ummar Palesdinu da Isra'ila suna matuka kaunar kungiyarsa ta Barcelona, don haka yana fatan wannan ziyara za ta taimakawa wajen samun zaman lafiya a tsakanin bangarorin biyu.

A daren wannan rana, a filin wasa na Bloomfiled dake birnin Tel Aviv, mutane fiye da dubu 15 sun kalli wasan horaswa na rabin awa, da kungiyar Barcelona ta baiwa matasa, da yaran Palesdinu da na Isra'ila a kyauta. Wadannan matasa da yara daga Palesdinu da Isra'ila sun halarci wasan horon ne bisa gayyatar da ma'aikatar bada ilmi ta kasar Isra'ila, da cibiyar shimfida zaman lafiya ta Shimon Peres suka yi musu. A cikin darasin, 'yan wasan kungiyar sun zama masu bada horo da koyar da fasahohin wasan kwallon kafa ga yaran. Daga bisa ni kuma suma sun gudanar da horo tsakaninsu. Cikin manyan baki da suka halarci dandalin wasan har da shugaba Peres na Israila.

1 2 3 4
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China