A shekarar 2009, an gudanar da gasar karo na farko a birnin Beijing dake kasar Sin, gasar da ta samu babbar nasara. Daga baya, aka sake gudanar da ita a shekarar 2011 da kuma 2012 a birnin Beijing. Bisa yarjejeniyar da aka daddale a tsakanin Sin da Italiya, za a gudanar da gasar a shekarar 2013 ko 2014 a kasar Sin. Sabo da haka, batun ko za a sake yin gasar a birnin Beijing ko a'a, ya jawo hankalin masu sha'awar wasan kwallon kafa na kasar Sin kwarai da gaske.
A ranar 27 ga wata, hukumar kawancen wasan kwallon kafa ta kasar Italiya ta tsaida kudurin gudanar da wannan gasa ta Super Cup ta bana a kasar Italiya. Zakara a gasar Serie A ta Italiya a karon da ya gabata wato kungiyar Juventus, da zakarar gasar Italian Cup kungiyar Lazio ne za su taka leda a gasar ta Super Cup a filin wasa na Olympics, dake birnin na Rome a ranar 18 ga watan na Agusta. (Zainab)