in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nocerino na iya barin AC Milan, a cewar manajan sa
2013-07-19 16:55:53 cri
Wasu rahotannin baya bayan nan na nuna cewa dan wasan tsakiyan nan na kulaf din AC Milan dake kasar Italiya Antonio Nocerino, na iya barin kulaf din nasa zuwa Inter Milan. Manajan wannan dan wasa Marco Sommella ne ya bayyanawa wata kafar watsa labaran wasanni hakan, dai dai lokacinda Nocerinon ke kokarin samun tasiri a fagen taka leda ga kulaf din na AC Milan.

A cewar Marco Sommella, muddin dai dan wasan da yake wakilta ya gaza samun damar taka leda yadda ya dace a kulaf din nasa na yanzu, to ba shakka zasu dubi yiwuwar sauyawa zuwa wani kulaf din na daban, watakila su waiwayi Inter Milan, koda yake kawo yanzu basu fara Magana da kulaf din na Inter ba, amma Sommella na ganin daga yanzu zuwa watan Satumba mai zuwa suna iya yin hakan. Manajan na Nocerino ya kara da cewa abu mafi muhimmanci ga dan wasan shi ne, ya samu damar buga kwallo cikin walwala, idan kuwa hakan ta gagara, to fa babu abinda ya rage illa neman sauyi. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China