in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Lionel Andres Messi:babban jagoran kungiyar Barcelona
2013-08-10 16:28:04 cri


A yau za mu mai da hankali ne ga fitaccen dan wasan kwallon kafan kasar Argentinan nan, wanda ke taka leda a Kulaf din Barcelona na kasar Sifaniya wato Lionel Andres Messi, inda za mu kalli matsayinsa a cikin kungiyarsa ta Barcelona.

A hakika, wasu na ganin cewa shi Lionel Messi ya kasance babban jagora ga kulaf din Barcelona musamman a wannan lokaci, wanda matsayinsa ya kasance mai muhimmancin gaske, da ya dara ma na mai horar da 'yan wasan kungiyar.

Hakan zai dada bayyana a fili idan aka dubi kalaman Gerardo Daniel Martino, sabon mai horar da 'yan wasan kungiyar ta Barcelona daga kasar Argentina. Wanda a lokacin da ya karbi mukamin horas da kulaf din a ranar 23 ga watan Yulin bana, ya bayyana cewa, in ba domin Lionel Messi ba, da bai samu damar zama babban mai horar da 'yan wasan kungiyar ba, a cewarsa dukkan al'ummar Argentina ya kamata su nuna godewa Messi.

Ta la'akari da batun Martino, za mu iya ganin cewa, nasarorin da Messi ya samu a kungiyar Barcelona, sun wuce batun girmamawa, ko alfahari kawai, a'a har ma da cikakken ikon fada a ji, don haka ne ma ake kiransa babban jagoran kungiyar Barcelona.

Idan mun yi bincike kan tarihin wannan kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, za mu ga yadda kungiyar ta gamu da matsaloli da yawa sakamakon koma baya da dan wasan ta Ronaldinho ya gamu da su, daga bisani Josep Guardiola, babban mai horar da 'yan wasan kungiyar a lokacin, ya yi kwaskwarima ga tsarin kungiyar, inda ya canza matsayin Messi daga bangaren dama zuwa tsakiyar fili, ta haka ne kuma sannu a hankali ya mai da shi jagoran 'yan wasa.

Matakin da Guardiola ya dauka ya dace, domin in ba dan hakan ba, da an salwantar da kwarewar wannan fitaccen dan wasa, ganin yadda ya taba samun lambar yabo ta Ballon d'Or har sau 4. Lamarin da a wani lokaci hamshakin dan kasuwan kasar Sifaniya, kuma shugaban kulaf din Real Madrid Florentino Pérez yake ce, bambancin dake tsakanin kungiyarsa ta Real Madrid da kungiyar Bacelona shi ne lionel Messi.

A lokacin da 'yan wasan kungiyar Barcelona ke buga kwallo bisa shirin da mai horar da 'yan wasan ya tsara, Messi ne ke zama jagora. Kana idan kungiyar ta tsunduma cikin mawuyacin hali, to, Messi ne ke zama fita daga halin da a kan fuskanta, da zarar ya karbi kwallo nan da nan al'amura kan canza sau da dama shi ke warware matsala da kulaf din ke fuskanta. Guardiola ya taba bayyana cewa, Michel Jordan shi ne babban dan wasan da ya kafa tarihin jagorantar wasan kwallon kwando, yayin Lionel Messi ya kasance Michel Jordan a fannin wasan kwallon kafa. A cewarsa, kalilan ne daga 'yan wasa za su iya kama irin rawar da Messi da Jordan ke takawa, musamman a fagen wasan da suka shahara.

Guardiola ya yi kokari wajen tsara wata dabarar wasa, da ta tanaji sanya sauran 'yan wasan kungiyar kewaye Messi, tsarin da keda taken 4-6-0 wanda babu dan wasan gaba a cikinsa. Amma ta wannan tsari ne kungiyar Barcelona ta lashe FC Santos da ci 4 da nema, a gasar cin kofin duniya na manyan kuloflika da ta gudana a shekarar 2011, matakin da ya baiwa kulaf din Barcelona lashe wannan kofi. A yayin gasar, an sanya fitattun 'yan wasa kamar su Andrés Iniesta, Sergi Busquets, Xavier Creus, Francesc Fabregas, domin su kewaye Lionel Messi, ta yadda aka baiwa Messi damar nuna cikakkiyar kwarewarsa wajen sarrafa kwallo,da kuma dabararsa ta bada kwallo ga sauran 'yan wasa.

Bayan da Tito Vilanova ya maye gurbin Guardiola, a matsayin mai horar da 'yan wasan Barcelona, ya ci gaba da mai da Messi ginshikin kungiyar. A kakar wasa ta bara zuwa ta shekarar 2013 nan da muke ciki, Barcelona ta zama zakara a gasar La Liga, inda Messi ya ci kwallaye 46, ya kuma tallafa aka ci kwallo 12, jimilar da ta kai rabin yawan kwallayen da kungiyar ta ci.

Jaridar AS ta kasar Safaniya ta taba bayani kan kulaf din FC Barcelona, inda cewa, idan har za a iya samun wani dan wasa tauraro daya, wanda zai iya jefa kwallaye 91 a raga cikin shekara guda, to ba shakka dukkan sauran 'yan wasa za su rika dogaro da shi.

A shekarar 2012 data gabata, Lionel Messi ya ci kwallaye 91, inda ya kafa wani sabon matsayin bajinta a duniya, lamarin da ya sanya matsalar 'dogaro kan Messi' ta tsananta matuka. Har aka fara tambayar shin ban da Messi, wadanne 'yan wasa ne a kulaf din na Barcelona za su iya cin kwallo?

Idan an duba lissafin yawan kwallayen da aka ci, za a gano wannan batu ba abin mamaki ba ne. Alal misali, a shekarar 2012, Messi ya ci kwallaye 79 a kungiyar Barcelona, yayin da Xavier Creus da Francesc Fabregas suka kasance biye da shi da kwallaye 11. Sa'an nan, Alexis Sanchez ya samu kwallaye 10, Pedro Ledesma da Cristian Tello kowanensu ya samu kwallaye 9, David Villa Sánchez ya samu 8, yayin da Andrés Iniesta ya samu 7.

1 2
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China