Da yake jawabi a yayin wani taron gangami na siyasa a garin Chinhoyi mai nisan kilomita 115 arewa maso yamma da birnin Harare, shugaba Mugabe ya ce kada kasar Amurka ta yi karambanin gayawa kasar Zimbabwe yadda za ta gudanar da zabe.
Shugaban mai shekaru 89 na cikin jerin wadanda kasar Amurka ta dorawa takunkumi, tun 2001, kuma yana neman ya ci gaba da kasancewa kan kujerar mulki da ya yi shekaru 33 a kai, wato tun bayan da kasar ta samu 'yancin kai daga Burtaniya a 1980.
Mugabe ya ce, bisa dukkan alamu Amurka tana hauka, tana da tabin hankali idan har Ventrel ya bada shawarar cewa kada a yi zabe bayan karewar wa'adin 'yan majalisa, saboda wai wasu jam'iyyu na ganin cewa babu sauyi a kafofin watsa labaru da hukumomin tsaro.
A ranar Talatar wannan mako, mai Magana da yawun kasar Amurka Patrick Ventrel ya ce kasar Amurka ta damu matuka dangane da rashin fayyace komai game da shirin zabe a kasar Zimbabwe na ranar 31 ga watan Yuli, tare kuma da yin kira ga gwamnati da ta tabbatar an gudanar da zaben cikin adalci da kwanciyar hankali.
Wannan kira kamar nanata kira ne da tsohon abokin hamayyar Mugabe kuma Praministan kasar Morgan Tsvangirai yayi, wanda wannan ne karo na uku da yake takarar kujerar shugaban kasar tun 2002. (Lami)