in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zabukan kasar Zimbabwe zasu taimaka wajen kyautata yanayin tsaron shiyyar, in ji kasar Afrika ta Kudu
2013-07-26 15:35:14 cri
Nasarar tabbatar da zabuka yadda ya kamata a kasar Zimbabwe za ta taimaka wajen kara kyautata matsalar siyasa da tsaro a wannan shiyya, kamar yadda wani babban jami'in kasar Afrika ta Kudu ya bayyana a ranar Alhamis.

Wannan zai samar da yanayi mai kyau wajen bunkasa zaman al'umma da tattalin arziki, da zasu taimaka wajen kara kyautata zaman rayuwar al'ummar kasar Zimbabwe da na shiyyar baki daya, in ji mataimakin ministan harkokin kasa da kasa, Ebrahim Ebrahim, a yayin wani taron manema labarai a birnin Pretoria.

An tsaida shirya gudanar da zabukan kasar Zimbabwe a ranar 31 ga watan Yuli mai zuwa, shugaban kasar mai barin gado Robert Mugabe wanda zai fafata tare da Morgan Tsvangirai na jam'iyyar kawo sauyi na demokaradiya, kuma faraminstan kasar na yanzu. Haka kuma akwai wasu 'yan takara uku na daban da su ma za su fafatawa a cikin wannan zaben shugaban kasa.

A makon da ya gabata, zaman taron musammun na manyan jami'ai da na kungiyar SADC sun nuna yabo ga gwamnatin kasar Zimbabwe bisa gayyatar mambobin kungiyar SADC da su tura jami'an sa ido kan zabuka da kuma yadda tawagar ta samu tabo mai kyau daga wajen hukumomin kasar Zimbabwe. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China