Wata sanarwa daga ma'aikatar harkokin wajen Angola ta bayyana cewa tawagar ta sauka kasar Zimbabwe ne tun ranar Alhamis 18 ga wata, karkashin jagorancin Sandro de Oliveira, daraktan ofishin kungiyar SADC dake karkashin ma'aikatar wajen Angola, za kuma ta nazarci yadda zaben da ake fatan kadawa ran 31 ga wata zai wakana.
Jimillar jami'an dake kunshe cikin tawagar jami'an da zasu yi aikin sa ido ga zaben dake tafe, karkashin kungiyar habaka ci gaban kasashen Kudancin Afirka ta SADC dai yanzu haka sun kai 235, ana kuma sa ran wannan adadi ya kai mutum 300 nan da lokacin fara gudanar da zaben. (Saminu)