Yayin zaben dake tafe shugaba Mugabe zai fafata da tsohon dan hamayyarsa, kuma firaministan kasar Morgan Tsvangirai, wanda ke sahun gaba wajen yawan magoya baya a cikin dukkanin 'yan takarar da zasu shiga zaben.
A wani ci gaban kuma mataimakin shugaban hukumar zaben kasar ZEC Mr. Joyce Kazembe, ya tabbatar da tantance masu sa ido daga ketare har mutum 1,500, mafiya yawansu daga kungiyar AU, da kungiyar habaka yankin Kudancin Afirka ta SADC, da kuma 'ya'yan kungiyar hadin kan kasuwannnin Gabashi da Kudancin Afirka.
Bugu da kari gwamnatin kasar ta ki amincewa da bukatar Amurka, da kuma kungiyar tarayyar Turai, na sanya ido ga gudanar zaben, tana mai cewa kasashen yammaci da suka kakabawa kasar takunkumi, ba zasu yi mata adalci yayin da suke sanya ido ga gudanar zaben ba. (Saminu)