Shugaban kwamitin kungiyar Madam Nkosazana Dlamini Zuma wadda ta bayyana hakan ga manema labarai tace kungiyar ta yaba kwarai da cigaban da ake samu ya zuwa yanzu dangane da shirye shiryen da ake yi na zaben a kasar ta Zimbabwe.
Madam Dlamini Zuma wadda ta isa birnin Harare a ranar laraba sannan kuma ranar alhamis ta gana da dukkannin 'yan takarar Shugaban kasar su uku wato Shugaba mai ci yanzu Robert Mugabe,da Firaministan kasar Morgan Tvsangirai da kuma Kisinoti Mukwazhe.
Har ila yau ta gana da mataimakin Firaministan kasar Arthur Mutambara da kuma hukumar zabe na kasar,inda tayi bayanin cewa kungiyar ta yaba da yanayin da ta gani ya zuwa yanzu kuma tana rokon hakan zai dore ko da bayan zaben a tsakanin al'ummomin kasar,inda ta shawarci jam'iyyun da ba su samu nasara ba bayan zaben da su guji ta da zaune tsaye, maimakon haka su shigar da kara kotu.
Madam Zuma ta kuma tabbatar da cewa tsohon Shugaban kasar Nigeriya Olusegun Obasanjo zai isa kasar ta Zimbabwe a ranar asabar din nan mai zuwa 27 ga wata domin jagorantar tawagar mai mutane 60 na wakilan kungiyar AU masu sa ido a zaben. (Fatimah Jibril)