in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'an rundunar 'yan sanda a Zimbabwe sun fara kada kuri'unsu
2013-07-15 10:31:56 cri

Rahotanni daga Zimbabwe na bayyana cewa, dubban jami'an rundunar 'yan sandan kasar, da ma'aikatan zabe sun fara kada kuri'unsu, gabanin fara ayyukansu na musamman, yayin babban zaben kasar dake tafe ran 31 ga watan nan na Yuli.

Hukumar gudanar da zaben kasar ZEC ce ta tabbatar da hakan, tana mai cewa kimanin mutane 87,000 ne za su kada kuri'unsu a wannan dan tsakani, wandanda akasarinsu jami'an rundunar ta 'yan sanda ne. An kuma tanadi rumfunan zabe 209 a dukkanin fadin kasar domin gudanar da wannan muhimmin aiki.

Wannan zabe karon farko, na zuwa ne gabanin babban zaben da zai fidda sabon shugaban kasar ta Zimbabwe, da 'yan majalissu sama da 200, da kuma 'yan majalissar zartaswar kananan hukumomi kimanin 2,000, wadanda za su jagoranci kasar nan da shekaru 5 masu zuwa. Manazarta harkokin siyasa dai na ganin fafatawa a zaben shugaban kasa tsakanin shugaba Robert Mugabe dake kan karagar mulki, da dadadden dan adawarsa, kuma firaministan kasar Morgan Tsvangirai ce za ta fi daukar hankali yayin babban zaben.

Tuni dai jagororin biyu da rikicin zaben shekarar 2008, ya sabbaba shigarsu gwamnatin hadaka, a yanzu haka suka shiga yakin neman zabe kamun-da-na'in.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China