Labarin da aka samu ya sheda cewa, wannan tawagar dake karkashin jagorancin tsohon shugaban kasar Najeriya Olusegun Obasanjo za ta isa kasar Zimbabwe kwanaki 10 kafin kada kuri'ar babban zabe a kasar. Kafin haka kuma, wata karamar tawagar AU ta mutane 9 ta riga ta je kasar.
Yayin da babban zabe ke karatowa, jam'iyyun hamayya da kungiyoyi masu kare hakkin bil adama sun yi kira ga kungiyar tarayyar kasashen Afirka da kungiyar raya kasashen kudancin Afirka da su kara taka rawa, don magance aikata magudi da aikace-aikacen nuna karfin tuwo.
A nata bangaren kuma, hukumar 'yan sandan kasar Zimbabwe ta yi alkawarin cewa za ta girke jami'an tsaro a dukkan mazabun kasar don tabbatar da kwanciyar hankali a lokacin babban zaben.
An taba samun tashe-tashen hankula da zubar da jini yayin da aka gudanar babban zabe a kasar Zimbabwe a shekarar 2008. A shekarar 2009, an kafa gwamnatin hadaka a kasar wadda ta ci gaba da mulki har zuwa yanzu.
A babban zabe mai zuwa, shugaba mai ci Robert Mugabe mai shekaru 89 a duniya da abokin hamayyarsa kuma firaministan kasar, Morgan Tsvangirai za su sake takara da juna don neman kujerar shugaban kasa. (Bello Wang)