A wannan rana, jam'iyyar kawancen al'ummar Afirka ta kasar Zimbabwe wato Zanu-PF dake karkashin jagorancin shugaba Mugabe ta gudanar da yakin neman zabe na masu goyon bayanta a birnin Harare, babban birnin kasar. Mugabe ya bayyana wa masu goyon bayansa cewa, ba za a canja lokacin gudanar da zaben shugaban kasar ba wato ranar 31 ga wata da babbar kotun kasar ta tsaida. Shugaba mai shekaru 89 da haihuwa ya kara da cewa, idan kungiyar raya kasashen kudancin Afirka wato SADC ta tsoma baki kan zaben shugaban kasarsa, to kuma kasar za ta janye daga kungiyar.
A ranar 4 ga wata, babbar kotun kasar Zimbabwe ta ki amincewa da rokon gwamnatin kasar na jinkirta gudanar da zaben shugaban kasar, kuma ta tsaida kudurin gudanar da zaben a ranar 31 ga wata da shugaba Mugabe ya sanar. Kafin wannan, jam'iyyar adawa ta kasar da kungiyar SADC sun bukaci Mugabe da ya gabatar da rokon jinkirta zaben domin ba a shirya zabe sosai ba. (Zainab)