Mai magana da yawun fadar shugaban kasar Mac Maharaj ne ya bayyana hakan cikin wata sanararwa da ya fitar a ranar Litinin, biyowa bayan ziyarar da shugaban kasar Jacob Zuma ya kaiwa Mr. Mandela a asibitin da yake kwance.
Da yake tsokaci ga manema labarai bayan ziyarar da ya kai ga tsohon shugaban, Zuma ya yi kira ga masoya da masu fatan alheri ga Mandela, da su ci gaba da gudanar da addu'o'i kamar yadda suka saba.
Yanzu dai kwanaki 44 ke nan da kwantar da Mandela a asibiti, kuma wannan sanarwa ita ce ta farko tun bayan wadda aka fitar ranar bikin cikarsa shekaru 95 da haihuwa, wadda ke kunshe da ra'ayin fadar gwamnatin kasar dangane da halin da yake ciki.
Bugu da kari shima wani jika ga tsohon shugaban kasar mai suna Mandla, ya bayyana yadda Mandelan ke dada samun sauki, yana mai cewa hakan wani lamari ne mai matukar karfafa gwiwa.(Saminu)