Mai magana da yawun fadar shugaban kasar Mac Maharaj ya bayyana cewa ana yi wa Mandela jiyyar cutar sanyi ta pneumonia kuma har yanzu babu wani canji a jikin nasa tun bayan bayani da aka bayar ranar Lahadi.
Ya ci gaba da cewa, iyalansa sun kasance tare da shi a wannan rana kuma suna nuna godiya dangane da irin goyon baya da jama'a ke ba su.
Mandela wanda yanzu shekarunsa na haihuwa sun kai 94, an sake kwantar da shi a asbiti ne ranar 28 ga watan Maris saboda cutar hakarkari da ta sake taso masa.
Wannan shi ne karo na biyu da aka kwantar da Mandela a cikin wata guda. Ranar 9 ga watan Maris an kwantar da Mandela a wani asibiti a birnin Pretoria don binciken lafiyarsa a matsayin matakin lura da yanayin jikinsa saboda shekarunsa. Kashegarin wannan rana aka sallame shi. (Lami Ali)