Shugaba Zuma ya yi wannan jawabi ne a ranar Laraba 17 ga wata, ta bakin kakakinsa Mac Maharaj, inda ya taya daukacin al'ummar kasar murnar zagayowar wannan rana ta kasa da kasa da ake kebe, domin tunawa da irin gudummawar da Mandela ya baiwa rayuwar al'umma, tare da fatan cimma dukkanin kyawawan burikan da aka sanya a gaba, gabanin mintina 67 da za a shafe ana gudanar da ayyukan tallafawa rayuwar al'umma a ranar Alhamis.
Mandela wanda zai cika shekaru 95 a bana, zai yi bikin ranar haihuwarsa na wannan shekara ne a gadon asibiti, sakamakon wata cutar huhu da yake fama da ita tsahon lokaci. (Saminu Alhassan Usman)