Ta bayyana hakan ne bayan sanarwar da shugaban kasar Jacob Zuma yayi ranar Alhamis cewa Mandela na samun sauki amma dai har yanzu yana cikin yanayi mai tsanani.
Iyalan Mandela sun nuna farin ciki ganin cewa, tsohon shugaban na ci gaba da samun saukin rashin lafiyar tasa idan aka kwatanta da kwanaki kadan da suka wuce, inji Winnie a garin Soweto, dake kudu maso gabashin birnin Johannesburg, kamar yadda hukumar watsa shirye-shiryen kasar (SABC) ya bayyana.
Winnie tace, ita ba likita ba ce, to amma bisa abin da idanunta suka nuna mata, yana samun sauki fiye da kwanan baya.
A ranar Jumma'a Mandela ya cika kwanaki 21 a asibiti, inda ake mar jiyya saboda cutar huhu. Wannan shi ne lokaci da ya fi dadewa a asibiti bayan kwantar da shi da aka yi a watan Disamba.
Babbar 'yar Mandela, Makaziwe ta bayyanawa hukumar watsa shirye shiryen kasar Afirka ta Kudu ran Alhamis cewa, lokacin da suke wa Mandela magana, ya yi kokari ya bude idanunsa, sannan yana iya sanin duk sanda aka taba jikinsa.(Lami Ali)