yayin da yake magana da kafofin watsa labaru a ranar 21 ga wata, Jika ga tsohon shugaban mai suna Ndaba Mandela ya ce halin da Mista Mandela ke ciki na kyautatuwa, kuma yana sa ran ganin fitowarsa daga asibiti, labarin da ya kwantar da hankalin jama'ar kasar Afirka ta Kudu. Amma a nasa bangaren, rediyon CBS na kasar Amurka ya ba da labarin cewa, Mandela ya yi kwanaki da dama bai bude idonsa ba, kuma ba ya iya fayyace abubuwan da ke faruwa a kusa dashi. Dangane da wannan batu, Mac Maharaj, kakakin fadar shugaban kasar Afirka ta Kudu, ya ce ofishinsa ne kadai ke iya sanar da hakikanin yanayin da Mandela ke ciki, domin duk wani rahoto daga ofishin ana samun shi ne daga likitan Mista Mandela.'Har ila yau yace don kare sirrin Mandela da na iyalansa, gwamnatin kasar ba ta da sha'awar bayyana cikakken halin da yake ciki a yanzu.
A baya ma dai, rediyon CBS ya ba da labarin cewa, da sanyin safiyar ranar 8 ga wata, yayin da ake kokarin kai Mista Mandela zuwa asibiti, motar dake dauke da shi ta gamu da matsala, matakin da ya sanya Mandelan kasancewa a gefen hanya har mintuna fiye da 40, kafin daga bisani a kawo wata motar data karasa da shi asibiti. Dangane da wannan labari Mista Maharaj ya ce hakikanin gaskiya hakan ya auku, sai dai ya kara da cewa, motar da ta gamu da matsala na dauke da na'urorin janya masu inganci, tare da wasu kwararrun jami'an lafiya dake tare da Mista Mandela a lokacin, don haka ya samu kulawar da ta dace, don magance ci gaba da tsanantar yanayin da yake ciki. (Bello Wang)