in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An sake kwantar da Mandela asibiti saboda sake tasowar cutar huhu
2013-03-29 10:52:15 cri
Ran 27 ga wata da daddare bisa agogon wurin, an kai tsohon shugaban kasar Afirka ta Kudu Nelson Mandela asibiti bayan cutar huhun da yake fama da ita ta sake taso masa.

A kwanan baya, an taba kwantar da Mandela a asibiti a lokuta da dama don masa jiyya ko duba lafiyarsa, inda lamarin ya janyo hankulan jama'ar kasar sosai saboda damuwa da suke yi da lafiyar jikin tsohon shugabansu.

Cikin wata sanarwar da fadar shugaban kasar Afirka ta Kudu ta bayar, an ce, ran 27 ga wata da daddare, an kai Mr. Mandela wani asibitin da ke babban birnin kasar na siyasa, Pretoria don samar masa jiyya saboda sake tasowar cutar huhu.

Kakakin fadar shugaban kasar Mac Maharaj ya bayyana wa kafofin watsa labarai cewa, lokacin da aka kai Mandela asibiti, yana cikin hayyacinsa.

A halin yanzu dai, ana jiyyarsa da kuma duba lafiyarsa a asibiti, kuma bisa labarin da aka samu, yana samun sauki. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China