in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana kula da lafiyar Mandela yadda ya kamata, in ji shugaba Zuma
2013-06-12 16:34:40 cri
A ranar Talata 11 ga wata, shugaban kasar Afirka ta Kudu, Jacob Zuma ya bayyana cewa, yanzu ana kula da lafiyar tsohon shugaban kasar Nelson Mandela dake kwance a asibiti yadda ya kamata, ko da yake cutarsa tayi tsanani sosai, duk da haka yana cikin hali mai kyau.

Ranar 11 ga wata, rana ce ta hudu da Mandela ya yi a asibiti. A wannan rana, yayin da yake magana da 'yan jaridan kamfanin watsa labaru na kasar Afirka ta Kudu, Zuma ya ce, ya yi hira da likita mai kula da Mandela a ran 10 ga wata, kuma ana ba shi jinya mai kyau yanzu, kuma ma'aikata suna iyakacin kokarin su, da fatan Mandela zai sami sauki da sauri.

Yayin da yake bayani game da cutar Mandela, Zuma ya ce, ko da yake cutarsa na da tsanani, amma yana cikin halin karko. Gwamnatin kasar Afirka ta Kudu ita ma ta fadi haka tun bayan da Mandela ya shiga asibiti.

Ban da haka, iyalan Mandela suna zuwa asibiti a koda yaushe domin kula da shi. Kafin wannan, an bada labarin cewa, iyalan Mandela sun ki amincewa da jami'an gwamnatin kasar da na jam'iyyar ANC su je asibiti domin gai da shi.

A cikin hirar dai Shugaba Zuma bai fadi lokacin da zai je asibitin ba.

A safiyar ranar 8 ga wata, an maida Mandela mai shekaru 94 da haihuwa wani asibitin dake birnin Pretoria cikin gaggawa a sakamakon kamuwa da cutar huhu. Wannan ne karo na uku da aka kwantar dashi a asibiti cikin shekarar nan. Gwamnatin kasar ta ce cutarsa na da tsanani sosai,wanda a da ba ta taba bayyana haka ba.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China