Bikin cika shekaru 95 na Mandela za'a yi shi a duniya baki daya ranar 18 ga watan Yuli, inda daya daga cikin abubuwan da za'a yi ya hada da kowa ya sadaukar da minti 67 kacal na wannan rana domin aiwatar da wassu ayyuka da zai samar da rayuwa mai kyau.
Babban jigon wannann biki na wannan shekara shi ne "Yaye Talauci".
Sello Hatang, babban shugaban cibiyar Nelson Mandela yana karfafa gwiwwar al'ummomi a ko'ina suke a duniya da su maida kowace ranar ta Mandela ta hanyar taimakawa marasa karfi.
Cibiyar ta ce, yana da kyau idan har jama'a za su iya sadaukar da mintuna 67 na hidimarsu a kowace rana ga al'ummomi marasa galihu don maida shi ranar Mandela.
Daya daga cikin jikokin Mandela Zondwa Mandela yayi kira ga al'ummomin duniya baki daya da su yi ayyukan da zai inganta rayuwar marasa galihu ta hanya mai kyau, yana mai cewa kakansa yana cikin wani mawuyacin hali amman yana samun sauki. Babban abin da ke tafiyar da kasar Afrika ta Kudu shi ne bayar da ilimi ga Yara.
Mukaddashin ministan ilimi Enver Surty ya yi kira ga al'ummomi da su yi koyi da Nelson Mandela a irin ayyukan shi na taimakon al'umma.(Fatimah Jibril)