in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar tarrayar kasashen Afrika ta AU ta nuna damuwar ta kan rikicin kasar Somalia
2012-01-18 16:36:52 cri
Shugaban kwamitin kungiyar tarrayar kasashen Afrika  AU, Jean Ping ya nuna damuwar kungiyar a game da cacar baki a majalisar tarrayar ta rikon kwaryar a Somalia, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua ya sanar.

A cikin wata sanarwa da aka aikama kafofin watsa labarai a ranar Talata, shugaban kwamitin ya yi allah wadai da gagawar mambobin majalisar tarrayar ta rikon kwarya, da su ka kasa nuna dattaku, game da kalubalan da kasar ke fuskanta.

Ta wani bangare kuma, a cikin sanarwar ya jadadda cewa, zaben sabon kakakin majalisar, ya sabama yarjejeniyar Kampala ta watan Yuni na shekara ta 2011, da kuma matsayar da aka cimma a tautaunawa kan lamuran siyasa a watan Satumba na shekara ta 2011 a Mogadishu. Wadannan abubuwa za su kara rikitar da lamura bisa kan kokarin da ake na ci gaba wajen sasantawa da kawo zaman lafiya a Somalia.

Shugaban kwamitin ya yi kira ga mambobin majalisar tarrayar ta rikon kwarya da su hamzarta kan shawo wannan matsala ta cacar baki, ta hanayar yin aiki, da kuma darata abun da aka tsaida a taron Kampala. Haka ma kwamitin tsaro da zaman lafiya na kungiyar ya bukaci hakan a yayin taronsa da aka yi a ranar 5 ga watan Janairu na shekara ta 2012. (Abdou Halilou)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China