in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wani manzon MDD ya bukaci da a fadada aikin agajin da ake baiwa kasar Somaliya
2011-12-07 10:40:24 cri

A ranar talata 6 ga wata, kamfanin dillancin labaru na kasar Sin Xinhua ya ambato wakilin sakatare janar na MDD a kasar Somaliya Mr. Augustine Mahiga yana kira ga kasashen duniya dasu kara yawan tallafin jin kai da suke baiwa kasar Somaliya.

A cikin wata wasika da ya aikewa dukkan al`ummar kasar Somaliya kuma ya raba ta ga kafofin yada labarai, Mr. Mahiga ya ce duk da ana samun cigaba wajen rangwamen wahalhalu a tsakanin al`ummar kasar, amma akwai mutukar bukatar kasashen duniya su kara himmatuwa wajen kai dauki ga kasar, sanan kuma ya gargadi `yan kasar ta Somaliya dasu kaucewa duk wani abu da ka iya kawo cikas ga matakan tabbatar da zaman lafiya a yankin.

Wakilin na MDD ya cigaba da cewa ko kadan ba za a lamunci duk wani yunkuri da zai kai ga haifar da tawaya ga jadawalin matakan siyasa da aka dauka ba wajen samun dauwamammen zaman lafiya a kasar.

A dai cikin watan satunban wannan shekarar ce a birnin Mogadishu aka lasafta wasu mahimman matakai da za`a aiwatar kafin karshen wa`adin gwamnatin wocin gadin kasar a watan Agustan mai zuwa.

Matakan sun hada da batun tsaro, tsara daftarin kundin mulkin kasa, da sulhunta tsakani, wadannan kamar yadda Mr. Mahiga ya fada su ne zasu samar da ginshikin shugabanci nagari, a don haka ne ya bukaci hadin kan kowa da kowa domin kaiwa ga cimma wadannan burika.

Mr. Augustine Mahiga ya yi bayanin cewa yana da cikakken imanin da yawa daga cikin al`ummomin kasar da shugabannin kasar ta Somaliya suna son ganin wannan taswira da aka tsara ta kai ga tabbata.(Bagwai)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China