in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masu ruwa da tsaki a al'amuran kasar Somaliya sun rattaba hannu kan kawo karshen gwamnatin wucin gadi
2012-05-24 10:58:02 cri
A karshen ganawar da aka yi kan batutuwan da suka shafi kawo karshen gwamnatin wucin gadi a Somaliya, masu ruwa da tsaki a ranar Laraba 23 ga wata suka cimma yarjejeniyar kawo karshen gwamnatin rikon kwarya a kasar.

Wadanda suka rattaba hannu kan wannan yarjejeniya suka hada da Sheik Sharif Ahmed, shugaban gwamnatin rikon kwarya na kasar Somaliya da Abdiweli Mohammed Ali, firaministan gwamnatin rikon kwarya, da Sheik Hassan Sheik Aden, kakakin gwamnatin rikon kwaryan, da Abdirahman Mohamud Farole, shugaban yankin Putland da kuma Mahammed Ahmed Aalin, shugaban yankin Galmudug, har da wakilin Ahlu Sunna Waljama, sannan kuma da Augustine p. Mahiga wakilin MDD a kasar Somaliya. Wadannan mutane sun halarci wannan ganawar ne tsakanin ranakun litinin 21 zuwa laraba 23 ga watan nan da muke ciki a hedikwatar kungiyar tarayyan kasashen Africa AU dake birnin Adis Ababa na kasar Habasha.

Wadanda keda alhakin rattaba hannu kan yarjeniyoyin da suka shafi al'amuran kasar Somaliyan da suka hada da wakilin MDD sun rattaba hannun ne don samar da sararin cigaba da kawo karshen gwamnatin rikon kwarya a kasar Somaliya.

Wannan gwamnatin na rikon kwarya zai kawo karshen wa'adin ta nan da wata 3 wato a cikin watan Agusta mai zuwa.( Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China