Mataimakin ministan dangantakar kasa da kasa da hadin gwiwa Ebrahim Ebrahim shi ne ya yi wannan kira yayin da yake jawabi ga 'yan jarida a birnin Pretoria dangane da abubuwa dake wakana a fagen duniya. Ya yi suka kan harin da aka kaiwa ofishin MDD a kasar Somaliya ranar 19 ga watan Yuni 2013 wanda ya yi sanadin rayukan mutane 15 ciki har da 'yan Afirka ta kudu guda 2.
Ya ce abin bakin ciki ne ganin cewa kungiyar MDD wacce ke aikin kyautata zaman lafiya, zamantakewa da bunkasa tattalin arziki gami da tallafawa bil adama ga gwamnatin Somaliya da jama'ar kasar kansu, yanzu ta zamo a bar kaiwa hari.
Gwamnatin Afirka ta kudun na mai imanin cewa ofishin MDD a kasar Somaliya zai ci gaba da ayyukansa na tallafawa gwamnatin kasar da ma sauran jama'a duk da koma baya da aka samu sakamakon wannan hari.
Ya yi kira ga al'ummar duniya su baiwa gwamnatin somaliya goyon baya a kokarin kafa zaman lafiya da dorewar kasar. (Lami Ali)