An kammala aikin sauya dakarun sojojin kiyayen zaman lafiya na Sin a yankin Darfur na Sudan
A ranar 28 ga wata, sojojin kiyaye zaman lafiya da kasar Sin ta tura zuwa yankin Darfur na kasar Sudan karo na 8 sun kammala sauyin ayyuka da 'yan uwansu, da za su komo gida cikin tawaga ta 7, a sansanin sojojin kiyaye zaman lafiya na M.D.D..Bayan da suka kammala sauyin aikin, wadannan sojojin kiyaye zaman lafiya na rukunoni guda 2 za su gudanar da atisayen soji da dama cikin hadin-gwiwa, sannan kuma sabuwar rundunar kiyaye zaman lafiyar za ta fara gudanar da aikinta yadda ya kamata.
Kungiyar sojojin kiyaye zaman lafiyar karo na 8 da Sin ta tura ga yankin Darfur na Sudan ta kunshi da rukunonin gine-gine guda 2, darukunin aikin ba da tallafi, guda daya da daya na kula da kiyaye zaman lafiyar jama'a da daya na aikin jinya, kuma za a jibge su a birnin Nyala da ke kasar Sudan, za kuma su gudanar da aikin gine-gine, da daidaita batutuwa cikin gaggawa da aikin jin kai da sauransu, kuma za su shafe watanni 8 suna gudanar da wannan aiki.(Bako)