A ranar Jumma'a 14 ga wata, kwamitin sulhu na MDD yayi suka da kakkausar murya dangane da hari da aka kai wata ma'ajiyar MDD dake jihar Kordofan a kasar Sudan.
Wata sanarwa da kwamitin mai mambobi 15 ta bayar na bayyana cewar mambobin kwamitin sulhu sun yi suka kan hari da aka kaiwa dakarun tsaron MDD a Abyei (UNISFA) da kuma wanda aka kai a hedkwatar shirin hadin gwiwa na sa ido da tantancewa na kan iyaka (JBVMM), dake Kadulgi a Sudan, a ranar 14 ga watan nan.
A fadin sanarwar, harin ya yi sanadin mutuwar ma'aikacin kiyaye zaman lafiya daya, dan asalin kasar Habasha kana mutane biyu sun samu rauni.
Mambobin kwamitin har wa yau a cikin sanarwar sun nuna jimaminsu ga iyalan wanda aka kashe a harin, gwamnatin kasar Habasha da kuma UNISFA.
Sun kuma yi kira ga gwamnatin kasar Sudan da ta dauki matakin yin binciken lamarin da kuma hukunta wadanda suka aikata.
Mambobin kwamitin sulhun har wa yau sun jadadda cikakken goyon bayansu ga dakarun na MDD tare da yin kira ga dukkan bangarori da su maida wukarsu kuma bada cikakken hadin kai ga cibiyoyin domin a samu nasarar aiwatar da ayyuka.
Hakazalika, babban sakataren MDD Ban Ki-Moon a ranar Jumma'a shima ya bukaci gwamnatin kasar Sudan da dakarun SPLM na shiyyar arewa da su dakatar da fada da juna, su maido da yarjejeniyar tsagaita bude wuta don a samu kawo karshen rikici a yankin kudancin Kordofan da jihar Blue Nile.(Lami Ali)