in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sakataren MDD ya yi matukar Allah wadai da kisan jami'an wanzar da zaman lafiya a Abyei
2013-05-05 15:52:20 cri
Babban magatakardar MDD Ban Ki-Moon ya yi matukar Allah wadai da kisan wasu jami'an wanzar da zaman lafiya, ranar Asabar a yankin Abyei, yankin da kasashen Sudan da Sudan ta Kudu ke takaddama a kansa.

Cikin wata sanarwar da kakakinsa ya fitar, Mr. Moon ya yi tir da wannan hari, wanda dakarun Misseriya suka kaiwa tawagar UNISFA, lamarin da ya sabbaba kisan babban jagoran al'ummar Ngok Dinka mai suna Dengkuol Deng, tare da wani jami'in tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD, baya ga wasu abokan aikinsa biyu da aka ce su ma sun samu munanan raunuka.

Babban magatakardar majalissar ta dinkin duniyar ya kuma yi kira ga kasashen Sudan, da makwafciyarta Sudan ta Kudu, da ma kabilun Ngok Dinka da Misseriya, da su kai zuciya nesa, su kuma kaucewa daukar matakan da za su iya rura wutar rikicin da ya auku. Aukuwar wannan lamari, a cewarsa ya dada nuna irin matukar bukatar da ake da ita ta kafa hukumomin wucin gadi, da za su jibinci ci gaba da shawarwari, don gane da matsayin karshe ga yankin na Abyei, kamar dai yadda yarjejeniyar ranar 20 ga watan Yunin shekarar 2011 ta tanada. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China