Al-Bashir ya baiyanawa wani taron majalisar Shura ta jam'iyyar National Congress Party mai mulki ranar Jumma'a cewa Sudan ba za ta bari man fetur din kasar Sudan ta kudu ya wuce ta tekun kasar Sudan ba sai har in Sudan ta kudun ta dakatar da goyon baya da take baiwa 'yan tawaye da kuma aiwatar da dukkan yarjejeniya da suka kulla tsakaninsu baki daya.
Ya ci gaba da cewa Sudan na da cikakken bayani dangane da goyon baya da Sudan ta kudu ke baiwa kungiyar 'yan tawayen Revolutionary Front Alliance.
Hankali ya kara tashi a kasashen Sudan da Sudan ta kudu bayan da shugaba Omar Al-Bashir ya sanar a watan Mayu cewa za'a dakatar da fitar da man kasar Sudan ta kudu ta cikin yankunan kasar Sudan, inda ya bada misali da tunzura 'yan tawaye da Juba take yi game da kasar Sudan.
A kuma ranar Lahadi, Sudan ta baiyana cewa ta amince da shawarwari da kungiyar tarayyar kasashen Afirka AU ta gabatar wanda ke da nufin kawo kareshen tashin hankali tsakanin Sudan da Sudan ta kudu.
A baya bayan nan bangarorin biyu sun amince da maido da fitar da man fetur daga Sudan ta kudu a matsayin hanyar aiwatar da yarjejeniyar hadin gwiwa da kasashen biyu suka rattaba hannu a kai a birnin Addis Ababa na kasar Habasha cikin shekarar da ta wuce. (Lami Ali)