Yau Alhamis 27 ga wata da safe, da misali karfe 11, shugabar kasar Korea ta kudu Park Geun-hye ta iso birnin Beijing, domin fara ziyararta na tsawon kwanaki hudu a kasar Sin.
Wannan ya kasance karo na biyu da Park Geun-hye ta kai ziyara a kasashen ketare bayan hawanta mukamin shugabar kasar. Shugabannin kasashen biyu za su yi ganawa bayan da suka zama sabbin shugabannin kasashensu. Manyan shugabannin kasar Sin Xi Jinping, Li Keqiang, Zhang Dejiang ne za su gana da ita.
Jigon ziyarar Park Geun-hye a wannan karo shi ne "kara kwarin gwiwa" domin bayyana burinta na kara amincewa juna a tsakaninta da shugabannin kasar Sin da kuma zurfafa dangantakar hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare tsakanin kasashen biyu.
Manazarta sun nuna cewa, babban batun da za a tattauna a yayin ziyararta a wannan karo shi ne kawar da makaman nukiliya a zirin Korea, kana kasa da kasa na sa ran cewa, kasashen biyu za su cimma kyakyawar matsaya kan batun. (Amina)