in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka da Korea ta kudu ba za su ban hakuri ga Korea ta arewa a barazanar da take yi musu ba
2013-05-08 15:12:57 cri

Shugaban kasar Amurka Barack Obama da takwaransa na kasar Korea ta kudu Madam Park Geun-hye sun bayyana a ran 7 ga wata cewa, ba za su yi hakuri da baranazar da tsokana da Korea ta arewa take yi musu ba, tare kuma da yin kira ga Korea ta arewa da ta maido da tuntuba da kasahen duniya da kuma daukar matakai da suka dace domin samun taimako yadda ya kamata.

Bayan da shugabannin biyu suka gana da juna a fadar White House, Barack Obama ya shedawa manema labarai cewa, Korea ta arewa ta sha kaye a kokarinta na lalata dangantakar dake tsakanin Amurka da Korea ta kudu ko kuma samu girmamawa daga kasa da kasa. Ya kara da cewa, kasashen biyu na fatan kara tuntubar Korea ta arewa ta bin hanyar diplomasiyya, da kuma samun amincewa da juna a nan gaba bisa sharadin cewa, ya kamata Korea ta arewa ta dauki matakai da suka dace, da kuma cika alkawarinta na kawar da makaman nukiliya a zirin Korea.

Shugaba Park Geun-hye ita ma ta nuna cewa, ta yarda da kara matsin lamba kan Korea ta arewa a fannin makamai ciki hadda makaman nukiliya.

A nata gefen kasar Sin ta bakin kakakin ma'aikatar harkokin wajen ta Hua Chunying ta nuna cewa, tana fatan bangarori daban-daban da wannan batu ya shafa za su dauki matakai da suka dace domin tabbatar da zaman lafiya da sassauta halin da ake ciki a wurin.

In ji ta, kasar Sin na fatan bunkasuwar dangantakar dake tsakanin Amurka da Korea ta kudu za ta yi amfani ga tabbatar da zaman lafiya da karko a zirin. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China