in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Korea ta Arewa ta sanar da rashin amincewarta kan yarjejeniyar kawar da makaman nukiliya tsakaninta da Korea ta Kudu
2013-03-08 16:50:36 cri

Kamfanin dillancin labarai na kasar Korea ta Arewa KCNA ya ba da labari a yau Jumma'a 8 ga wata cewa, kwamitin dinkin kasa cikin lumana na Korea ta arewa ya sanar a wannan rana da cewa, kasar za ta soke dukkannin yarjeniyoyi da ta kulla tare da Korea ta kudu dangane da rashin kai wa juna hari, tare kuma da sanar da rashin amincewa kan yarjejeniyar kawar da makaman nukiliya a zirin Korea, kana za ta rufe hanyar tuntubar juna tsakaninsu ta wurin Panmunjom.

Sanarwar ta ce, Korea ta kudu ta yi atisayen soja tare da Amurka wanda ya kasance matakin kai hari a fili, ya kuma karya yarjejeniyar rashin kai wa juna hari.

Saboda haka, Korea ta arewa ta ce ba za ta amince da wannan yarjejeniya ba, wato tun daga lokaci da aka daina amfani da yarjejeniyar daina yaki a Korea ta arewa a ranar 11 ga wata. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China