Sanarwar ta ce, wadanda suka ci karensu ba babbaka a wannan yanki sun hada da masu ayyukan fashin teku, masu hare-hare da makamai, masu sumogar miyagun kwayoyin da sauransu, inda wadannan abubuwa suka kawo barazana ga tsaro a kan hanyoyin jiragen ruwa, da kuma kawo illa ga zaman lafiya da karko da bunkasuwar tattalin arzikin wannan yanki.
Saboda haka, kasashen da dama a wannan yanki, sun lashi takobin yin hadin kai domin daukar matakai da suka dace wajen yaki da laifuffuka da za a aiwatar a kan teku.
Dadin dadawa, wannan sanarwa ta yi kira ga MDD da kungiyar tarayyar Afrika da su ba da taimako da ya wajaba ga kasashen wannan yanki wajen yaki da laifuffuka a kan teku. (Amina)