in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan sama jannati a cikin kumbo Shenzhou-10 na kasar Sin sun ba da lacca karo na farko a sararin samaniya
2013-06-20 16:05:25 cri

Safiyar yau 20 ga wata, 'yan sama jannati a cikin kumbo Shenzhou-10 na kasar Sin suka fara ba da lacca a sararin samaniya cikin nasara, sun bayyana yadda abubuwa suka kasance a cikin kumbo Tiangong-1.

'Yar sama jannati Wang Yaping ta ba da lacca, Nie Haisheng kuwa ya ba da taimako, Zhang Xiaoguang kuma ya dauki hoton bidiyo.

A cikin darasi mai tsawon mintoci 40, 'yan sama jannati sun yi aikin gwaje-gwaje na kimiyya da fasaha, tare kuma da yin musayar ra'ayi ta wayar bidiyo tare da dalibai da malamai dake doron kasa.

Dalibai kimanin 330 sun shiga ajin wannan darasin, ciki hadda daliban kananan kabilu, daliban manoma 'yan kwadago da dai sauransu, ban da haka, dalibai kimanin miliyan 60 daga makarantu dubu 80 sun kalli shirin ta TV da aka gabatar kai tsaye.

Wani masani ya ce, wannan ne karo na farko da aka ba da lacca ta sararin samaniya, abin da ya bayyana matsayin da aka cimma na gudanar da aikin nazarin sararin samaniya domin horar da dalibai. Hakan ya karawa matasa kwarin gwiwa wajen koyon ilmin kimiya da fasaha da kuma nazarin sararin samaniya har ma da abubuwa da ba a taba tabo shi ba. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China