A ranar 16 ga wata ne, aka harba kumbon Shenzhou-9 da ke dauke da 'yan sama jannati 3 a cibiyar harba tauraron dan Adam na Jiuquan da ke yankin arewa maso yammacin kasar Sin, domin gudanar da aikin hada shi da kumbon Tiangong-1 a sararin samaniya. A yayin da suka zirga-zirga a sararin samaniya ne, 'yan sama jannati suka yi nasarar hada Kumbon Shenzhou-9 da na Tiangong-1 da hannu, waje guda kuma abin da ya nuna cewa, Sin ta mallaki wannan muhimmiyar fasaha a fannin zirga-zirgar sararin samaniya.(Bako)