in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta harba kumbon "Shenzhou mai lamba 10" a tsakiyar watan Yuni
2013-06-03 16:15:33 cri
Kakakin hukumar ayyukan harbar kumbunan dake daukar dan Adam zuwa sararin samaniya ta kasar Sin ya sanar a ranar 3 ga wata cewa, kasar Sin za ta harba kumbon "Shenzhou mai lamba 10" zuwa sararin samaniya a tsakiyar watan Yuni, tare da 'yan sama jannati 3 wadanda za su hade da kumbon "Tiangong mai lamba 1".

A wannan rana, an kai kumbon "Shenzhou mai lamba 10" a kan roka samfurin "Changzheng-2F" daga yankin nazari fasaha na cibiyar harbar tauraron dan Adam zuwa sararin samaniya ta Jiuquan zuwa yankin harbar kumbuna. Wannan ya bayyana cewa, an shiga matakin karshe na harbar kumbon "Shenzhou mai lamba 10".

Bisa labarin da aka bayar, an ce, bayan da aka yi nasarar harbe shi, kumbon zai hade da kumbon "Tiangong mai lamba 1"da aka harba a shekarar 2011, da fara yin gwajin kimiyya a sararin samaniya. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China