Yauzu Sin ta shirya sosai a yankin Si Zi Wang Qi dake jihar Mongoliya ta gida mai saukar Shenzhou-9 saboda aka yi nasarar hade kumbunan Shenzhou-9 da Tiangong-1 da hannu waje guda a karo na farko, inda za a yi gaggarumin bikin maraba da dawowar 'yan sama jannatin uku da kumbon.
Tsarin da za a yi amfani da shi wajen karbar kumbon Shanzhou-9 ta zama wani muhimmin mataki na aikin nazarin ilimin zirga-zirgar sararin samaniya, ya hada da kasu biyar, wurare biyu da kumbon zai sauka,wani wurin saukar kumbo na wucin gadi, rukunin ceton gaggawa a doron kasa da teku, masu ba da jiyya ga 'yan jannati. Kumbunan shenzhou-1 zuwa 8 dukkansu, sun dawo doron kasa ne a wannan wuri. Masu kula da wannan aiki sun isa yankin Si Zi Wang Qi tare da yin aikin share fage. Ya zuwa yanzu, an shirya sosai a wurin.(Amina)