Bayan da kumbon nan mai taken Shenzhou mai lamba 8 ya sauka a kasa, ma'aikata sun fara bincike kan iskar da ke ciki da wasu kananan halittun da kumbon ke dauke da su, haka kuma an cire wata na'urar kiwon halittu da kasashen Sin da Jamus suka hada kai wajen kera ita daga cikin kumbon. Bayan haka, babban jami'i mai jagorar aikin zirga-zirgar kumbo mai dauke da 'yan saman jannati a kasar Sin, Chang Wanquan ya sanar da nasarar da aka samu wajen gudanar da aikin hadewar kumbon Tiangong mai lamba 1 da na Shenzhou mai lamba 8. (Bello Wang)