in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi shiri cewa kumbon shenzhou-9 zai sauka a ranar 29 ga wata
2012-06-28 16:07:19 cri

A ran 28 ga wata, kakakin cibiyar kula da harkokin kumbon da ke dauke da dan Adam zuwa sararin samaniya ya sanar da cewa, bisa shawarar da cibiyar ba da umurni game da aikin hada kumbon dake dauke da mutane na Tiangong-1 da na Shenzhou-9 ta yanke, an ce, kumbon Shenzhou-9 zai sauka a ranar 29 ga wata da karfe 10 da safe.

A ranar 28 ga wata da karfe 9 da mintin 22, dan sama jannati Liu Wang ya raba kumbon Shenzhou-9 da na Tiangong-1 da hannu, kuma wannan shi ne karo na farko da aka cimma nasarar raba kumbon Shenzhou da wani kumbo da hannu.

Babban kwamandan da ke kula da 'yan sama jannati na Sin Chen Shanguang ya ce, yayin da kumbunan ke zirga-zirga a sararin samaniya, an gudanar da aikin bincike game da harkokin likitanci a sararin samaniya kamar yadda aka tsara, kuma an samu samakamo mai gamsarwa. Bayan binciken da za a yi a nan gaba, za a yi amfani da adadin da aka samu wajen bin bahasin raya likitanci a sararin samaniya don tabbatar da lafiyar 'yan sama jannati ta yadda za su iya aiki cikin kumbuna a sararin samaniya cikin dogon lokaci.

Bayan da aka raba kumbon Tiangong-1 da na Shenzhou-9 cikin nasara, kumbon Tiangong-1 ya kama wata hanya ta daban, don gudanar da wani aiki na daban, kuma nan gaba za a hada shi wani kumbo daban.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China