Hukumar kula da hasashen yanayi ta kasar Sin da cibiyar sa ido game da yanayin zirga-zirgar sararin samaniyya sun yi hasashe cewa, daga ranar 27 zuwa ranar 28 ga wata, za a yi ruwan sama tare da walkiya a wurin da kumbon Shenzhou-9 zai sauka, haka kuma daga ranar 29 ga wata, za a samu gajimare da hasken rana. Haka kuma, wani jami'in kula da hasashen yanayi a hukumar kula da harkokin hasashen yanayi ta jihar Mogonliya ta gida ta Sin ya ce, yanayi a wurin da kumbon Shenzhou-9 zai sauka ya dace da yanayin saukar kumbo.(Bako)