in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan sama jannati 3 sun fita daga kumbon Shenzhou-9
2012-06-29 11:38:00 cri

A ranar 29 ga watan Yuni da karfe 11 na safe, bayan da kumbon da ke dauke da mutane na Shenzhou-9 ya sauka a jihar Mongoliya ta gida cikin nasara, 'yan sama jannati Jing Haipeng, Liu Wang, da Liu Yang suna cikin koshin lafiya, kuma sun fita daga cikin kumbon a karkashin taimako na ma'aikata.


Bayan da 'yan sama jannati 3 suka fita daga cikin kumbon, suna cikin koshin lafiya, kuma sun yi murmushi, tare da gai da ma'aikata a wurin. A ranar 16 ga wata ne, aka harba kumbon Shenzhou-9 da ke dauke da 'yan sama jannati 3 a cibiyar harba tauraron dan Adam na Jiuquan da ke yankin arewa maso yammacin kasar Sin, domin gudanar da aikin hada shi da kumbon Tiangong-1 a sararin samaniya. 'Yan sama jannati suka samu nasarar hada Kumbon Shenzhou-9 da na Tiangong-1 da hannu, kuma abin da ya nuna cewa, Sin ta mallaki wannan muhimmiyar fasaha a fannin zirga-zirgar sararin samaniya.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China