A ranar 29 ga wata da tsakar rana, bayan da kumbon da ke dauke da 'yan sama jannati na Shenzhou-9 ya sauka lami lafiya a jihar Mongoliya ta gida da ke yankin arewacin kasar Sin, 'yan sama jannatin 3 sun fita daga cikin kumbon, kuma suna cikin koshin lafiya. Kasar Sin ta cimma burin kammala aikin hada kumbunan da ke dauke da mutane cikin cikakkiyar nasara.
Firaministan kasar Sin Mr. Wen Jiabao ya je cibiyar kula da zirga-zirgar sararin samaniya ta birnin Beijing, inda ya karanta sakon taya murna da kwamitin tsakiya na J.K. ta Sin da majalisar gudanarwa da kwamitin soja na gwamnatin ta kasar Sin suka bayar, inda aka yi murna ga nasarar da aka samu ta hada kumbon Tiangong-1 da na Shenzhou-9 a sararin samaniya waje guda, kana Mr. Wen ya nuna babban yabo game da wannan lamari.
Shugabannin kasar Sin Wen Jiabao, He Guoqiang, Zhou Yongkang da sauransu sun kalli halin dawowar kumbon Shenzhou-9 zuwa doron kasa a cibiyar kula da zirga-zirgar sararin samaniya ta Beijing.
A ranar 16 ga wata da dare ne, aka harba kumbon Shenzhou-9 a cibiyar harba tauraron dan Adam na Jiuquan da ke yankin arewa maso yammacin kasar Sin, domin gudanar da aikin hada shi da kumbon Tiangong-1 da hannu a sararin samaniya.
Haka kuma, Mr. Wen ya kara da cewa, kammala aikin hada kumbuna a sararin samaniya ya nuna cewa, an samu ci gaba a fannin hada kumbunan a sararin samaniya, kana abin da ya nuna cewa, kasar Sin ta samu muhimmin ci gaba cikin matakai na 2 wajen inganta aikin harba kumbunan dake dauke da mutane a sararin samaniya.
Bisa matakai 3 da ke kunshe cikin shirin dabarun inganta aikin kumbunan dake dauke da mutane zuwa sararin samaniya na Sin, an ce, ya zuwa shekarar 2020, kasar Sin za ta kafa tasha a sararin samaniya. Haka kuma, mallakar fasahar hada kumbuna da hannu ya kasance wani muhimmin ci gaba cikin mataki na 2, muddin aka mallaki wannan fasaha, za a aza wani harsashi mai kyau wajen kafa tasha a sararin samaniya da raya aikin kumbunan dake dauke da mutane a sararin samaniya.
Kasar Sin ta kasance kasa ta uku a duniya da ta mallaki wannan fasaha a duniya bayan kasashen Amurka da Rasha. (Bako)