Ranar 11 ga watan dai itace rana ta karshe ga aikin na rajista, kuma kafin kammala wannan aiki, babban wakilin kwamitin shawarwari kan batun nukiliya na Iran, kana sakataren kwamitin koli na tsaron kasar, Saeed Jalili, da tsohon ministan harkokin waje na kasar, Ali-Akbar Velayati, da tsohon shugaban kasar, Akbar Hashemi Rafsanjani, da babban mai ba da shawara ga shugaban kasar Iran, Esfandiyar Rahim-Mashaei dukkansu sun ziyarci ma'aikatar harkokin cikin gida domin yin rajistan shiga takarar.
Bisa labarin da aka bayar, an ce, bayan kammala wannan aiki, kwamitin sa ido kan kundin tsarin mulkin kasar ta Iran, zai fara yin bincike kan 'yan takarar, kuma zai gabatar da takardar sunayen 'yan takara ta karshe nan da makwanni biyu masu zuwa.
Za a gudanar da babban zaben kasar Iran ne dai a watan Yuni dake tafe.(Fatima)