Ministan tsaron kasar Amurka Chuck Hagel ya isa kasar Isra'ila a ran 20 ga wata, domin fara ziyararsa a yankin gabas ta tsakiya na tsawo mako daya. Wannan ya kasance karo na farko da ya kai ziyara a Isra'ila tun fara aikinsa a wannan mukami, muhimmin batun da za a tattauna a kai shi ne yadda kasashen biyu za su tinkari batun nukiliyar kasar Iran.
Hagel ya bayyana a wannan rana cewa, barazanar da kasar Iran ta yi wa Amurka da Isra'ila daya ce, abin da ya sa, kasashen biyu ke da matsaya daya a kan batun nukiliyar kasar Iran, don haka ra'ayinsu ya zo daya kan batun kawar da makaman nukiliya daga kasar Iran, sai dai kuma ra'ayinsu ya bambanta dangane da lokacin da za su kai farmaki kan Iran. Hagel ya jaddada cewa, dole ne, Isra'ila ta yanke shawara da kanta kan matsalar ko za ta dauka ko kuma yaushe ne za ta daukar matakan soja irin na kashe biri kafin ya yi barna kan kasar Iran. (Amina)