A cikin sanarwar, an dora muhimmanci sosai game da shirin nukiliya na kasar Iran, da bukatar Iran da hukumar IAEA da suka yi hadin gwiwa daga dukkan fannoni, da gaggauta cimma matsaya guda tsakaninsu don daddale wasu yarjejeniyoyi da aiwatar da su a tsanake.
Bayan taron, wakilin kasar Iran a hukumar IAEA ya fada wa manema labaru cewa, cikin shekaru 10 da suka gabata, hukumar IAEA ba ta gano wata shaidar dake nuna cewa, Iran na habakar makaman nukiliya, kuma Iran tana fatan yin shawarwari game da fasahohi da hukumar IAEA, amma bai kamata hukumar IAEA ta sanya siyasa ba a yayin da take gudanar da aikinta.(Bako)