in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta fara gyara tashar wutar lantarki mafi girma ta kasar Nijeriya
2011-11-11 10:51:06 cri

A ran 10 ga wata, an fara aikin gyara tashar ba da wutar lantarki da karfin ruwa mafi girma ta Kainji ta kasar Nijeriya a jihar Niger, wanda cibiyar tsara fasali ta kamfanin samar da wutar lantarki ta hanyar yin amfani da karfin ruwa na kasar Sin da kuma kamfanin samar da wutar lantarki ta hanyar yin amfani da iskar gas na birnin Ha'erbin su ka dauki nauyin aikin. Wannan aiki ya shaida cewa, kasashen Sin da Nijeriya sun kara yin hadin gwiwa a fannin samar da wutar lantarki ta hanyar yin amfani da karfin ruwa.

Mai kula da wannan aiki na kasar Sin Sha Bin ya bayyana a gun bikin fara aiki cewa, tashar wutar lantarki ta Kainji dake jihar Niger ita ce mafi girma a kasar Nijeriya, tana taka muhimmiyar rawa wajen samar da wutar lantarki ga kasar, kasar Sin ta dora muhimmanci sosai kan wannan aiki. Kuma kasar Sin ta riga ta tura kwararru da dama zuwa kasar Nijeriya domin yin bincike da tattaunawa, ta yadda za a gyara wannan tashar wutar lantarki domin biyan bukatun jama'ar kasar Nijeriya a fannin wutar lantarki.

Babban jami'in tashar wutar lantarkin ta Kainji ta kasar Nijeriya R.O.Akinwumi ya ce, gwamnatin kasar Nijeriya ta dora muhimmanci sosai kan wannan aiki, yana fatan kwararrun kasar Sin za su yi kokarin farfado da wannan tashar wutar lantarki domin kawo moriya ga jama'ar kasar Nijeriya.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China