in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutum 1 ya rasa ransa sakamakon fashewar wasu na'urorin a wata tashar nukiliya ta kasar Faransa
2011-09-13 10:02:27 cri

Ranar Litinin 12 ga wata, bisa labarin da kafar yada labaru ta kasar Faransa ta bayar, an ce, mutum 1 ne ya rasu yayin da wasu 4 suka raunana sakamakon fashewar na'urori a tashar nikiliya ta Marcoule dake kudancin kasar.

Bisa labarin da aka bayar an ce, wannan hadari ya afku ne da misalin karfe 11 da mintoci 45 da safe. 'Yan sanda da 'yan kwana-kwana na wurin sun isa wuri nan da nan, yanzu an killace wannan tashar. Na'urorin da suka fashe na cibiyar wannan tashar wadda suke karkashin jagorancin wani kamfanin wutar lantarki na kasar Faransa.

Kwamitin nukiliya na kasar Faransa (CEA) ya ce ,ya zuwa yanzu, ba a samu tururin nukiliya ba.(Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China