in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Akwai yiwuwar lalacewar tukunya ta 3 ta tashar nukiliya na Japan
2011-03-25 16:45:37 cri

A ran 25 ga wata, hukumar tsaro ta makamashin nukiliya ta kasar Japan ta fayyace cewa, akwai yiwuwar lalacewar tukunya ta 3 ta tashar nukiliya dake tsibirin Fukushima na kasar Japan, abin da ya sa yawan burbushin nukiliya da aka samu a cikin ruwan dake tashar ya ninka sau dubu 10 idan aka kwatanta da na kullum.

A sa'i daya kuma, sakatare janar na kasar Japan Edano Yukio ya bayyana a wannan rana cewa, a sakamakon habakar burbushin nukiliya da rashin kayayyakin masarufi, watakila zai sa gwamnatin kasar Japan ta janye mazauna wurin dake da nisa kilomita 20 ko 30 daga tashar nukiliya. Ban da haka kuma, Edano Yukio ya yi kira ga mazauna da su janye da kansu, kuma ya bukaci gwamnatin wurin ta shirya sosai kan wannan batu.

Ya zuwa ran 25 ga wata da karfe 11 na safe, yawan mutanen da suka mutu a sakamakon bala'in girgizar kasa da na tsunami a kasar Japan ya kai 10066, a yayin da mutane 17452 suka bace. Kungiyar IMF ta duniya ta bayyana a ran 24 ga wata cewa, yawan kudin da kasar Japan ta yi hasara ya kai kashi 3 zuwa 5 cikin dari na yawan GDP na kasar, wanda ba zai kawo babbar barazana ga tattalin arzikin duniya ba.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China