Tun bayan da aka sake samar da wutar lantarki ga jerin na'urori lamba 2 da 5, ma'aikata sun farfado da tsarin samar da wutar lantarki na jerin na'urori lamba 1 da 6 na tashar farko, kuma za a sake farfado da tsarin samar da wutar lantarki na sauran jerin na'urori a kwanaki masu zuwa ba da dadewa ba, ta yadda za a sake yin amfani da na'urorin rage zafi. A game da haka, firaministan kasar Japan Naoto Kan ya ce, halin da ake ciki a tasoshin wutar lantarki na nukiliya ya samu kyautatuwa.
Amma sauran kasashen duniya sun nuna shakku ga kyautatuwar yanayin wadannan tasoshi. Babban darektan hukumar IAEA Yukio Amano ya nanata a gun taron musamman na manyan jami'an hukumar a ran 21 ga wata a birnin Vienna cewa, tashar farko ta wutar lantarki ta nukiliya dake tsibirin Fukushima tana cikin hali mai tsanani, amma muna iya ganin wasu kyakkyawar sakamakon da aka samu.(Lami)