in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Iran ta sanar da fara yin amfani da tashar nukiliya ta Bushehr
2011-05-19 10:31:59 cri

Ranar Laraba 18 ga wata a birnin Tehran, ministan harkokin waje na kasar Iran Ali Akbar Salehi ya sanar da cewa, kasar ta fara yin amfani da tashar nukiliya ta farko ta kasar wato tashar Bushehr.

Salehi ya ce, an yi amfani da kimiyya da fasaha mafi inganci domin gina wannan tasha, hakan ya sa ta zama tashar mafi samun tsaro da lafiya a duniya. Ban da wannan kuma, an kiyasta cewa, a cikin watanni biyu masu zuwa, yawan wutar lantarki da tashar za ta samar zai kai kashi 40 cikin 100 bisa na dukkansu da aka tsayar.

An ba da labari cewa, wannan tashar ta tsaya a wurin dake dab da birnin Bushehr wata tashar jiragen sama dake kudancin kasar, wadda ta kasance tashar ta farko na kasar, yawan wutar lantarki da wannan tashar za ta samar zai kai megawatt dubu daya.(Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China