Kamfanin Tokyo Electric Power ya sanar a ran nan da cewa, zai zub da irin wannan ruwan kimanin ton dubu 11.5 cikin teku, duk da cewa yawan tururin nukiliyar da ke ciki ya ninka abun da aka kayyade kimanin sau 100. Idan an samu damar shirya aikin yadda ya kamata, to, za a fara aiwatar da shi a ranar 5 ga wata.
A cewar Japan, gurbataccen ruwan da za a zubar da shi cikin teku ba zai haifar da babbar illa ga lafiyar dan Adam ba. Ko da a kan ci kifayen da aka kama daga wajen tekun da za a zuba gurbataccen ruwa a ko wace rana, to, yawan tururin nukiliya da ke tare da kifayen ba zai wuce wani ma'aunin da aka kayyade da zai iya kawo illa ba. (Bello Wang)